Shugaban ƴansandan Kenya ya yi murabus saboda mutuwar masu zanga-zanga

Spread the love

Sufeta-janar na ƴansandan Kenya ya ajiye muƙaminsa bayan makonnin da aka kwashe ana gudanar da zanga-zanga a ƙasar, lamarin da haifar da mutuwar mutane sama da 40.

Ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama sun zargi ƴansanda da harbin masu zanga-zanga, inda wasu suka mutu, sannan aka kama wasu ɗaruruwa.

Zanga-zanga ta ɓarke a Kenya a tsakiyar watan da ya gabata domin nuna adawa da shirin gwamnati na ƙara kuɗaɗen haraji.

Masu zanga-zanga sun kutsa cikin ginin majalisar dokokin ƙasar jim kaɗan bayan da ƴan majalisa suka amince da dokar mai cike da ruɗani.

Matakin da shugaban ƙasar William Ruto ya ɗauka na janye dokar ba ta sanya masu zanga-zangar sun saduda ba.

A ranar Alhamis shugaban ya sallamai da dama daga cikin ministocinsa inda ya sanar da shirinsa na kafa gwamnatin da za ta ƙunshi ɓangarori da dama.

Har yanzu akwai shirye-shiryen ci gaba da zanga-zangar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *