Shugaban Kungiyar Arewa Concerns Citizen For Development ACCD Amb. Comrade Dr. Rufai Mukhtar Danmaje ya yaba wa Shugaban Majalisar wakilai na Nigeria, Rt. Hon Tajudeen Abbas bisa jajircewarsa wajen kawo hadin kai da fahimtar juna da ci gaban kasa a majalisar,
Danmaje na cewar kamar yadda aka samu a zamanin sa biyo bayan majalisu guda goma da aka yi, kafin zuwan sa, wato an samu hadin kai mutika da fahimtar juna da kuma biyayya a tsakaninsu ‘yan majalisa da shuwagabanni, wanda hakan ya jawo ake ta gudanar da al’amuran hadewar kasa ne da dinke barakar tsakanin, wanda da can ba haka zaman tsarin zaman majalisa yake ba, yanzu an samu ci gaba mai kyau.
Wannan na zuwa ne a tattaunawar da Comrade Dr Rufai Danmaje ya yi da daraktan yada labaran ACCD Comrade Dahiru M. Maihula a Kano.
Dr Rufai ya ci gaba da cewa jama’a na iya bincika wa da kansu domin ganin irin yadda yake kokarin, kuma an sami nasara, da shi Shugaban Majalisa Rt. Hon. Tajudeen Abbas da fahimtar juna kan irin salon mulkinsa.
Daga karshe Shugaban Kungiyar Arewa ACCD ya yi fatan alheri ga kasa baki.
- Kowa na da damar sayen mai a matatar Dangote – NNPCL
- Zargin Ɓata suna: Tanimu Akawu ya nemi afuwar iyalan Ƙarƙuzu