Shugaban APC A Kano Abdullahi Abbas Da Fa’izu Alfindiki Sun Bayyana A Gaban Kotu Kan Zargin Batanci Ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Spread the love

Babbar kotun shari’ar addinin musulinci ta kasuwa, karkashin jaorancin mai shari’a Abdu Abdullahi Waiya, ta ci gaba da sauraren karar da aka shigar da shugaban jam’iyar APC reshen jihar Kano, Abdullahi Abbas da kuma tsohon shugaban karamar hukumar Birnin Kano, Fa’izu Alfindiki, kan zarginsu da yin maganganu na batanci ga gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.

A zaman kotun na yau wadanda ake karar ba su halacci zaman kotun ba, sai dai lauyan dake kare su, Barista Isma’il Abdul’aziz , ya shaidawa kotun cewa bata da hurumin sauraren karar.

A zaman kotun da ya gabata wadanda ake karar an gaza samun su don sada su da sammacin kotun, inda ta bayar da umarnin a sadar da su ta hanyoyin kafofin yada labarai dan asada zumunta.

Lauyan ma su kara Barista Shazali Muhammed Ashiru, ya mike da kotun ya roki kotun ta ba su wata rana don mayar da martani kan rokon kan  lauyan wadanda ake karar na cewa kotun bata da hurumin sauraren shari’ar.

Wasu yayan jam’iyar NNPP ne suka shigar da karar kan zargin da suke yi wa , Abdullahi Abbas da kuma Fa’izu Alfundiki da zargin batanci ga gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.

Haka zalika lauyan wadanda ake karar Barista Isma’il , ya kara da cewa sun yi suka ne kan rashin hurumin kotun saboda hanyoyin da aka bi wajen shigar da karar.

‘’ gaskiya daya daga cikin hujjar ta mu ma takamaimai mun kasa gane menene karar ta su kuma a cikin sammacin su karar ma bata tsaya ba, dan haka muna fatan kotun zata kori karar ‘’ Barista Isma’il Abdul’aziz’’.

Lauyan masu karar Barista Shazali Muhammed Ashiru, ya kara da cewa daman su fatan su wadanda ae karar su halacci zaman kotun kuma sun zo, don haka za su gabatar da hujjojinsu a zaman a gaba.

Alkalin kotun mai shari’a Abdu Abdullahi Waiya, ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Maris 2025, don bangarorin biyu su mayar da martaninsu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *