Shugaban Bankin Duniya Ya Ziyarci Masarautar Gaya.

Spread the love

Mai Martaba Sarkin Gaya Dakta  Aliyu Ibrahim Abdulqadir ya Karbi bakuncin  Shugaban Bankin Duniya Mr. Shubham Chaudhuri tare da Rakiyar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusif Wanda ya Samu Wakilcin Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi na Jihar Kano Hon. Umar Haruna Doguwa.

Da Yake Jawabi Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi na Jihar Kano Alhaji Umar Haruna Doguwa Ya Ce Sun Zo Fadar ta Gaya ne Domin Neman Tabarraki Sarki,Kasancewar Gaya gari ne me tsohon Tarihi.

Kwamishinan Ya kara da cewa  Mr . Shubham Chaudhuri yazo Kano ne Kwanaki uku da suka wuce dan duba Ayyukan da suka shafi Ilimin ‘Ya’Ya mata , Lafiya,har Noma da Sauransu,tare da yin alkawarin zai ci Gaba da Taimakawa Jihar Kano a fannoni daban daban dan ci gabanta.

Alhaji Umar Haruna Doguwa  Ya ci Gaba da cewa Mai Girma Gwamnan Jihar Kano ne Injiniya Abba Kabir Yusif ne  Ya umarci a Kawo shi Masarautar Gaya dan ai Masa Tarba Irin ta Sarauta.

Da Yake Gabatar da Jawabinsa Mr Shubham Chaudhuri ya ce sun zo Jihar Kano ne dan duba ayyukan da bankin Duniya Yake gudanarwa a  fannoni daban daban Na Jihar Kano, Ya Kuma Baiyana Jin dadinsa bisa gagarumar tarba da Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulqadir Ya yi Masa a Fadarsa.

Ina nan Daram a Jam’iyar PDP: Atiku Abubakar

Babu sahalewar Buhari a yawancin kuɗaɗen da CBN ya fitar – Fadar shugaban ƙasa

A inda a lokacin Ziyarar tasa ne ,Mai Martaba Sarki ya  Sa aka Shirya Masa Kwarya Kwaryar Hawan DABA . Domin Sada Zumunci da Kara Kulla  Alaka tsakaninsa da Masarautar Gaya.

A Jawabinsa Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulqadir Ya Baiyana bankin Duniya da cewa Tun tuni yake gudanar da Ayyukansa a Sassa daban daban Na ci Gaban rayuwar Al-uma a Fadin Kasar Nan.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *