Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya rasu a hatsarin jirgi

Spread the love

Jami’an Iran sun ce Shugaba Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen ƙasar, Hossein Amir-Abdollahian sun rasu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a wani yanki da ke kusa da kan iyaka da Azerbaijan.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an ga tarkacen jirgin a tsakanin wasu tsaunuka.

Shugaban ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran, Pirhossein Koolivand ya ce masu aikin ceto sun nufi wurin tarkacen jirgin amma babu alamar akwai waɗanda suka tsira.

JIrgin saman mai saukar ungulu na ɗauke ne da shugaba Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen ƙasar Hossein Amir Abdollahian.

Sauran waɗanda suke cikin jirgin sun haɗa da Ayatollah Mohammad Ali Al-e Hashem – limamin masallacin Juma’a na birnin Tabriz da Janar Malek Rahmati watau gwamnan lardin gabashin Azerbaijan.

Kwamandan askarawan kare lafiyar shugaban ƙasa, Sardar Seyed Mehdi Mousavi, da waɗansu jami’an tsaron na cikin waɗanda suka yi hatsari a jirgin mai saukar angulu.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani jami’in gwamnatin Iran na cewa jirgin ‘ya kone ƙurmus’.

Jirgin saman mai saukar ungulu ya faɗi ne a wani yanki mai tsaunuka mai nisa sosai kuma da farko aikin ceto shugaban ƙasar ya gamu da cikas sakamakon rashin kyawun yanayi da hazo.

Tun farko jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei ya yi kira ga mutanen da su yi wa dukkanin wadanda ke cikin jirgin addu’a.

Kawo yanzu ba a san musabbabin haɗarin jirgin sama mai saukar ungulun ba amma ɓangaren sufurun jirgin saman Iran ya fuskanci koma baya sakamakon takunkuman da Amurka ta sanya kasar.

Wane ne Ebrahim Raisi?

An kallonsa a matsayin wanda zai iya gadon jagoran addinin ƙasar Ayatollah Khamenei, a matsayinsa na mai tsattsauran ra’ayin siyasa.

An haife shi a shekarar 1960 a Mashhad inda masallacin ‘yan shi’a mafi tsarki yake, kuma ya bi sawun mahaifinsa ne wanda shi ma malamin addinin musulunci ne.

Ya bi sawun masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Shah wacce aka kifar a shekarar 1979.

Raisi, mai shekara 63, ya zama mataimakin mai shigar da ƙara a Tehran a lokacin yana da shekara 25.

Raisi ya bai wa masu hasashe mamaki a lokacin da ya tsaya takarar shugaban ƙasar a zaɓen 2017, inda ya zo na biyu a zaɓen.

A shekarar 2019, jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Khamenei ya bayyana sunansa a matsayin wanda zai jagoranci ɓangaren shari’ar ƙasar.

A watan Yunin 2021 ne aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar inda ya maye gurbin Hassan Rouhani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *