Shugaban Jami’ar MAAUN Farfesa Gwarzo, Ya Bayar Da Kyautar Motocin Aiki 2 Ga Ofishin Yan Sandan Hotoro Kano.

Spread the love

Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya yabawa shugaban jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria, MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, bisa gudunmawar motocin aiki guda Biyu, da ya bayar a ofishin Yan sandan Hotoro.

Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya yi wannan yabon ne, a Wata ziyarar bangirma da ya kai wa Farfesa Gwarzo, Wanda shi ne shugaban gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo (AAG).

CP Gumel, ya ce makasudin ziyarar ita ce mika sakon godiya ga Farfesa Gwarzo, bisa kyautar motocin aikin da ya bayar ga rundunar.

Kwamishinan Yan sandan ya kara da cewa, wannan Babban karamci ne kuma zai kara mu su, kwarin gwiwa wajen fadada sintiri a lungu da sako, musamman ma a yankin Hotoro da sauran wurare.

A bangaren kula da motocin Kwamishinan Yan sandan CP Gumel, ya tabbatar da cewa za a yi amfani da su, yadda yakamata da kuma kula da lafiyar motocin.

Kano CP lauds Prof Gwarzo for donating two operational vehicles to police

Majalisar koli ta addinin musulunci a Najeriya ta nuna damuwa kan makomar aikin Hajjin bana

Sai dai ya yi Kira ga sauran al’umma, musamman ma su hannu da shuni, da su yi koyi da Farfesa Gwarzo, wajen bai wa jami’an Yan sanda gudunmawar da za ta taimaka wa harkar tsaro.

Da yake nasa jawabin, Farfesa Gwarzo, ya bayyana Farin cikinsa matuka ga Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, bisa yaba masa da ya yi, sakamakon gudunmawar motocin da ya bayar, ya kuma yi alkawarin ci gaba da bayar da hadin kai domin inganta tsaron jahar Kano baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *