Daga: Aliyu Danbala Gwarzo.
Shugaban jamiyyar APC na karamar Hukumar Gezawa, Alhaji Sani Yamadi, ya ba da tallafi, yayin Taron saukar karatun Al Quran magirma a makarantar Tarbiyyatul Aulad dake Garin Jannarya a karamar hukumar Gezawa Kano.
Shugaban jamiyyar ya ce ya ba da Atamfofin Tare da kudin dinki naira Dubu Dari domin kara zaburar da daliban wajen ci gaba da kokarin zuwa makaranta domin samun ilimin Addini, kuma hakan zai sa sauran dalibai na baya sukara zage dantse wajen ci gaba da zuwa makaranta.
yakara da cewa “hakika irin wadannan Dalibai yadace ake kokarin taimakawa duba da yadda suka maida hankali wajen zuwa makaranta har Allah yabasu damar sauke Al Qurani mai girma, dan haka babu tukuicin da yakamata ayiwa Daliban sai da irin wanan tagomashi kuma ashirye muke mucigaba da tallafawa makaratun islamiyyu da dalibai a Gezawa baki daya.
Kazalika Yamadi ya yi kira ga matasa dasu maida hankali wajen neman ilimin Addini domin shine zai taimake su a duniya da lahira.
Daga karshe yayiwa wadannan dalibai fatan Alkairi tare da Fatan zasuyi amfani da abinda suka karanta domin samarwa da kansu gobe mai kyau.