Gamayyar kungiyoyin Matasa a Arewacin Najeriya sun kai ziyara ta musamman ga shugaban kamfanin SAGAMA Construction Ltd, SAGAMA Homes(Baban kamfanin gine gine da dlilacin gidace a tarayyar na Najeriya) Alhaji Ali Nuhu, a jihar Kano.
Ziyarar ta gudana kar kashin Jagorancin Comr. Aliyu Abdul Garo, da Fatima Joel Ajemasu, inda kungiyoyin suka mika shaidar girmamawa da yabo bisa irin gudunmawar da Alh. Ali Nuhu ke bayarwa wajen tallafawa matasan Arewacin Najeriya.
Shugabannin gamayyar kungiyoyin sun bayyana cewa manufar wannan ziyara ita ce nuna godiya da yabo bisa irin kokarin da shugaban kamfanin SAGAMA Homes ke yi wajen karfafawa matasa ta hanyar samar da ayyukan yi, horas da Matasa, da kuma inganta ci gaban tattalin arziki a yankin Arewa.
- Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Yi Taro Kan Tsaro Da Tattalin Arziƙi A Taraba
- Yan Sanda Sun Kama Wadanda AKe Zargi Da Satar Wayoyi 23 Da POS A Kano
Sun kuma bayyana cewa irin wannan jajircewar ‘Yan kasuwa masu kishin kasa yana da matukar tasiri wajen gina al’umma mai karko, tare da karfafa zumunci da hadin kai tsakanin shugabanni da matasa.
Kungiyoyin sun yi addu’ar Allah ya kara daukaka kamfanin SAGAMA Construction tare da ba shi ikon ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da taimako ga matasan Arewacin Najeriya da kasa baki daya.