Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Hon. Abdullahi Ghali Basaf Ya Kaddamar Da Fara Aikin Hanyar Chalawa- Kankare Zuwa Danjirima

Spread the love

Shugaban karamar hukumar Kumbotso, Hon. Abdullahi Ghali Basaf, ya kaddamar da fara aikin hanyar Chalawa zuwa Kankare har  zuwa Danjirima dake karamar hukumar a jihar Kano.

Hon. Ghali Basaf, ya wallafa hotuna da bidiyon fara kaddamar da aikin hanyar, a shafinsa na Facebook, a yau juma’a.

Tuni dai al’umar yankunan da aikin hanyar ya shafa suka bayyana farin cikinsu kan aikin raya kasar da shugaban karamar hukumar ya kawo musu.

Sun kara da cewa tunda ake yin shugabancin  karamar Kumbotso, ba a taba samun, mai hidimtawa al’ummarsa ba kamar Hon. Abdullahi Basaf.

A cewarsu sun kwashe shekaru suna ta kiraye-kirayen ayi musu aikin hanyar, amma babu wanda ya saurare su, sai a wannan lokaci da karamar hukumar ta samu hazikin shugaba.

Haka zalika sun yi kira ga gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya kara tallafa wa shugaban karamar da dukkan abinda ya zai taimaki al’ummarsa domin ba zai bashi kunya ba, mutun ne mai gaskiya da jajircewa da kuma rikon amana.

Mutanen Chalawa da makotansu da kuma masu ababen hawa , sunce matukar aka kammala aikin hanyar tattalin arzikin yankin zai kara habbaka da kuma kara samun aikin yi ga matasan yankin dari bisa dari.

A karshe sun yi addu’a ga shugaban karamar hukumar Allah ya taimakeshi dangane da abubuwan ci gaban da yake kawo wa karamar hukumar Kumbotso baki daya.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *