Shugaban karamar hukumar Nasarawa ya koma NNPP Kwankwasiyya a Kano

Spread the love

 

Shugaban Karamar hukumar Nasarawa Auwal Lawan Shu’aibu wanda aka fi sani da Aranposu ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyar NNPP mai mulkin jihar Kano.

Bayan ficewarsa Aranposu ya ce, Ungulu ta Koma gidanta na Tsamiya Kuma fa His Excellency “ABBA KABIR” Masoyin talakawa ne da Kano, mu ci gaba da taya shi da adu’a”.

Auwal Lawan ya bayyana hakan ne a sahihin shafinsa na Facebook a safiyar talatar nan.

Tun da sanyin safiya ne dai aka wayi gari da wasu hutunan shugaban karamar hukumar ta Nasarawa da gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya yin wata ziyara da ya kai masa.

Ba mu ne muka yi sanadin kaɗe saurayi da mota a Jibiya ba – Kwastam

Ƴansanda sun kama ‘masu garkuwa da mutane’ a Abuja

A hotunan an ga Aranposu sanye da jar hula Wanda hakan Ke nuni da cewa ya koma tafiyar Kwankwasiyya da ya bari tun lokacin da aka raba gari tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

Dama dai Aranposu ya yi kaurin suna wajen sukar dan takarar gwamnan jihar kano a jam’iyyar APC duk da sun fito a karamar hukuma guda.

Kwanaki kadan ne dai suka ragewa shugabannin kananan hukumomi a jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *