Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya yi wata gagarumar kora da kuma rage matsayin wasu manyan jami’an gwamnati saboda rashin katabus a wani muhimmin aikin raya kasa da ya basu.
Kafofin yada labaran kasar sun ce Mista Kim ya zarge su da sakaci da kuma janyo wa kasar asarar tumujin kudade a aikin mayar da garin Samjiyon wani wurin jan hankalin masu yawon bude ido na duniya.
Ya sanar da matakin ne yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai don ganin yadda abubuwa ke gudana.
Nan ne kuma mahaifar jatuminsa da ya rasu, wato Kim Jong-il.