Bassirou Diomaye Faye, ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Senegal na biyar.
An rantsar da shi ne a Dakar, babban birnin ƙasar.
A watan da ya gabata ne, Faye mai shekara 44 ya lashe zaɓ da kashi 54 cikin 100 na ƙuri’un da aka jefa inda ya zarce abokin hamayyarsa Amadou Ba.
A ranar Juma’a ne majalisar tsarin mulkin ƙasar ta tabbatar da Faye a matsayin wanda ya ci zaɓe.
Shugabannin ƙasashe daga nahiyar Afirka sun halarci bikin rantsar da shi har da shugaban Najeriya Bola Tinubu wanda shi ne shugaban ƙungiyar Ecowas.
- Farashin Kayayyakin Masarufi Na Ci gaba Da Tashi A Najeriya
- An kama mutum takwas da ake zargi da kisan malamin jami’a a Borno