Shugabannin duniya sun taya Pezeshkian murnar lashe zaɓen Iran

Spread the love

Wasu shugabannin duniya sun taya Masoud Pezeshkian murnar lashe zaɓen shugaban ƙasar Iran.

Shugaban China, Xi Jinping da na Rasha, Vladimir Putin sun ce suna fatan ƙulla alaƙa mai kyau da tsohon likitan zuciyar.

Shi kaɗai ne mai ra’ayin kawo sauyi da aka bai wa damar tsayawa takara a zaben na ranar Juma’a, kuma ya doke abokin karawar sa mai ra’ayin riƙau.

Bayan nasarar ta sa, Mr Pezeshkian ya ce akwai namijin aiki a gaban sa, na ceto Iran.

Ya yi alkawarin ƙulla sabuwar yarjejeniyar makamin nukiliya da ƙasashen Yamma da cire takunkumin Amurka da kuma kawar da ƙungiyar Hisba.

Amma jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei ne mai ƙarfin ikon yanke hukunci a kan duk wata doka ko zartar da wani tsari a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *