Shugabannin Kananan hukumomin jahar Kano guda 44 sun shigar da Gwamnatin jahar, kara a gaban wata babbar kotun tarayya a Abuja, kan yunkurin da gwamnatin ke yi na dibar kudin su dan gina wasu Gadoji guda 2.
Takardar Karar me Lamba FHC/ABJ/CS/1733/2023, Shugabannin Kananan Hukumomin sun yi Karar Gwamnatin Kano ne, Da Kwamishinan Shari’a Na jihar kano Dama Akanta Janar Na Kano.
Sun roki kotun a Kotu ta Hana gwamnatin yin tasarifi da kudadensu na cikin asusun hadaka da sukeyi da ita(Joint Account) ta kowacce fuska , sakamakon abinda suka ce ana kokarin dibar kudin a aikin gadojin da za a yi ta Dan Agundi da ta Tal’udu.
Kananan hukumomin sun hada da Ajingi, Albasu, Bagwai, Bebeji, Bichi, Bunkure, Dala, Dambatta, Dawakin Kudu, Dawakin Tofa, Doguwa, Fagge, Gabasawa, Garko, Garum Mallam, Gaya, Gezawa, Gwale, Gwarzo.
Sauran sune, Kabo, Kano Municipal, Karaye, Kibiya, Kiru, Kumbotso, Kunchi, Kura, Madobi, Makoda, Minjibir, Nasarawa, Rano, Rimin Gado, Rogo, Shanono, Sumaila, Takai, Tarauni, Tofa, Tsanyawa, Tudun Wada, Ungogo, Warawa, Wudil.
Tuni mutanen da suka fito daga Karkara suka nuna bacin ransu kan Gadojin da za a gina a iya kwaryar birnin Kano, ya yin da Manoma da yan kasuwar kauyuka ke dama da lalatattun hanyoyi sakamakon mayar da su saniyar ware.