Shugabannin kananan hukumomi uku sun fice daga APC zuwa NNPP mai mulkin Kano

Spread the love

Shugaban jam’iyar APC na kasa DR. Abdullahi Umar Ganduje, da kuma dan takarar gwamnan jahar a jam’iyar APC, DR. Nasiru Yusuf Gawuna, sun rasa shugabannin kananan hukumomin su bayan sun sauya sheka zuwa jam’iyar NNPP mai mulkin jahar Kano.

Shugabannin kananan hukumomi ukun da suka sauya sheka sun hada Hon. Mudassir Aliyu, shugaban karamar hukumar Garin Mallam, da kuma Hon. Ado Tambai Kwa shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa , wanda ya fito daga mazabar shugaban jam;iyar APC na kasa DR. Abdullahi Umar Ganduje.

Sai kuma shugaban karamar hukumar Nasarawa , Hon. Auwal Lawan Aramposu , wanda suke mazaba daya da dan takarar gwamna na jam’iyar APC a zaben 2023, DR. Nasiru Yusuf Gawuna.

Rundunar yan sandan Kano ta shirya tsaf don bayar da cikakken tsaro a ziyarar Uwar gidan shugaban kasa Oluremi Tinubu.

Na kamu da cutar tsananin damuwa bayan rabuwa da matata :Zango

Gwamnan jahar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf, ne ya karbi shugabanin kananan hukumomin uku da magoya bayan su, a gidan gwamnatin jahar Kano a ranar Asabar, inda ya tabbatar mu su cewa jam’iyyar NNPP za ta yi rawar gani wajen karbar sauran yayan jam’iyar APC don inganta rayuwar al’umma.

Gwamnan ya jadda kudirin gwamnatinsa na bunkasa tattalin arziki ta hnayar zuba jari a fannonin ilimi,kiwon lafiya, Noma, albarkatun ruwa da kuma karfafa zamantakewar jama’a.

Ficewar yayan jam’iyar APCn zuwa jam’iyar NNPP na zuwa ne makonni biyu kacal , da shugaban jam’iyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya mika wata budaddiyar wasika day a gayyaci shugabannin NNPP zuwa jam’iya mai mulki.

EFCC na neman matar Emefiele ruwa-a-jallo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *