Shugabar matan jam’iyar PDP shiyar Arewa maso yamma, Amb. Zainab Audu Bako, ta yi kira ga Gwamanan kano Alhaji Abba Kabir Yusif da yadawo Jam’iyar PDP.
Zainab Audu ta bayyana hakanne alokacin da take ganawa da manema labarai a ofishinta da kantitin Post Office,inda ta bayyana managartan halaye da gwamnan kanon yake da su tun yana kwamishina.
Inda takara da cewa a matsayinta itama ta tsohuwar kwamishina tasan irin jajircewarsa yanzu kuma gashi yana gwamna amma yana sanya kunnuwansa akasa domin jin al”umar da yake shugabanta.
Ta ce shugaba nagari yakamata asanshi don haka ya yi watsi da kiran zuwa APC tunda kuma jam’iyar NNPP ita kuma Rikici ya yi mata yawa don haka ya dawo PDP.
Ambassador zainab Audu Bako ita ce shugabar mata ta jahar kano , karkashin gamayyar jam’iyu ta IPAC inda takara da bayyana yanda mata yakamata su yi wajen shigowa harkokin siyasa domin IPAC tashirya tallafawa mata jajirtattu domin daukar nauyinsu.
- Jubilations As Kano State Police Command Arrests Suspected Kidnapper, Rescue A 75 Year Old Victim
- Ana Zargin Wani Matashi Da Kashe Saurayin Kanwarsa A Kano