Sifaniya ta zama ta farko da ta lashe gasar cin kofin nahiyar Turai karo hudu a tarihi, bayan da ta doke Ingila 2-1 ranar Lahadi.
A minti na uku da suka koma zagaye na biyu ne Sifaniya ta ci ƙwallo ta hannun Nico Williams, bayan da Lamine Yamal ya zura masa ƙwallon.
To sai dai Ingila ta farke ta hannun Cole Palmer, bayan da Jude Bellingham ya ajiye masa ƙwallon a kasa, saura minti 27 a tashi daga fafatawar.
Saura minti biyar a tashi daga karawar Sifaniya ta kara na biyu ta hannun Mikel Oyarzabal.
- NDLEA ta kama ƙwayoyin da aka yi yunƙurin safararsu zuwa Amurka ta Birtaniya
- An Harbi Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump
Da wannan sakamakon Sifaniya ta lashe Euro 2024, kuma na huɗu jimilla, ita ce kan gaba a yawan lashe kofin nahiyar Turai a tarihi.
Sifaniya, mai kofin duniya a 2010 ta fara ɗaukar kofin nahiyar Turai a 1964 da 2008 da 2012 da kuma yanzu a 2024 a Jamus.
Wannan shi ne wasa na 28 da suka kece raini a tsakaninsu a dukkan fafatawa, inda Sifaniya ta yi nasara 11 da canjaras hudu, Ingila ta ci 13.
Haka kuma Ingila ta zura ƙwallo 46 a raga, ita kuwa Sifaniya ta ci 34 jimilla.
Wasan karshe da suka fuskanci juna shi ne a Nations League a 2018, inda Sifaniya ta je Wembley ta ci 2-1, yayin da Ingila ta yi nasara da cin 3-2 a Sevilla.
Sai dai wasan karshe da suka kara a Euro shi ne a 1966, inda suka tashi 0-0, amma Ingila ta yi nasara cin 4-2 a bugun fenariti.
Wannan shi ne karo na biyu a jere da Ingila ta kai wasan karshe a Euro, bayan da Italiya ta doke ta a Euro 2020 a bugun fenariti a Wembley.
Haka kuma karon farko da Ingila ta yi wasan karshe a babbar gasa ba a gida ba, wadda take da kofin duniya a 1966, sai dai ba ta taɓa lashe Euro ba.
Wannan ita ce gasa ta 17 da aka kara a gasar cin kofin nahiyar Turai a tarihi.
Ƴan wasan Sifaniya da na Ingila da suka fara wasan
Sifaniya ta fara wasan da Dani Carvajal da kuma Robin le Normand, wadanda suka kammala hutun hukuncin dakatarwa.
Dani Olmo, wanda yana cikin ƴan wasa shida da suka ci ƙwallo uku-uku a Euro 2024, an fara karawar da shi tare da Alvaro Morata.
Haka kuma an fara da Lamine Yamal, wanda ya yi bikin cika shekara 17 da haihuwa ranar Asabar.
Ƴan wasa 11 na Sifaniya: Simon, Carvajal, Le Normand, Laporte, Cucurella, Rodri, Fabian, Yamal, Olmo, Williams, Morata.
Masu jiran ko-ta-kwana: Raya, Nacho, Vivian, Merino, Joselu, Torres, Grimaldo, Remiro, Baena, Zubimendi, Oyarzabal, Jesus Navas, Lopez.
Ita kuwa Tawagar Ingila canji ɗaya ta yyi daga 11 da take fara wasa da su, inda Luke Shaw ya maye gurbin Kieran Trippier.
Yayin da Harry Kane ke gurbin mai cin ƙwallo da taimakon Jude Bellingham da kuma Phil Foden.
Bukayo Saka yana daga gefen gaba da kuma Marc Guehi da John Stones da kuma Kyle Walker a gurbin masu tsare baya.
Ƴan ƙwallon Ingila 11: Pickford, Walker, Stones, Guehi, Saka, Mainoo, Rice, Shaw, Foden, Bellingham, Kane.
Masu jiran ko-ta-kwana: Alexander-Arnold, Trippier, Ramsdale, Konsa, Dunk, Gallagher, Toney, Gordon, Watkins, Bowen, Eze, Gomez, Henderson, Palmer, Wharton.
Jerin wadanda ke kan gaba a cin ƙwallaye a Euro 2024
- Dani Olmo Sifaniya ƙwallo uku
- Georges Mikautadze Georgia ƙwallo uku
- Cody Gakpo Netherlands ƙwallo uku
- Harry Kane Ingila ƙwallo uku
- Ivan Schranz Slovakia ƙwallo uku
- Jamal Musiala Jamus ƙwallo uku
Wadanda ke kan gaba a yawan lashe gasar cin kofin nahiyar Turai
2020 Italiya
2016 Portugal
2012 Sifaniya
2008 Sifaniya
2004 Girka
2000 Belgium
1992 Denmark
1988 Netherlands
1984 France
1980 Jamus
1976 Czechoslovakia
1972 Jamus
1968 Italiya
1964 Sifaniya
1960 Soviet Union