Sirika da ‘yar sa sun gurfana a kotu

Spread the love

An gurfanar da tsohon ministar sufurin jirgin sama Hadi Sirika da ‘yar sa Fatima a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda EFCC ke tuhumarsu da laifuka shida da ke da alaka da almundahana na kusan naira biliyan uku.

EFCC wadda ta shigar da karar na zargin ministar da amfani da mukaminsa ba bisa ka’ida ba ta hanyar ba da kwangilar naira biliyan daya da dubu dari uku domin kafa kamfanin Nigeria Air.

Tsohon ministan da ‘yarsa sun gurfana a kotun ne da misalin karfen 9 a yau ranar Alhamis tare da mutum na uku da ake zargi da hannu a lamarin, daga ciki har da Jalal Sule Hamma, wanda surukin Hadi Sirika ne.

Haka zalika a gurfanar da kamfanin Al Duraq Investment a gaban kotun inda aka tuhume shi da hannu a Almundahanar.

Sai dai dukkaninsu sun musanta laifukan da ake tuhumarsu da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *