Siyasa Da Tsaro: Gwamnan Kano Ya Tura Neman A Sauya Kwamishinan Yan Sandan Jihar.

Spread the love

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nemi shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya gaggauta cire kwamishinan ‘yan sandan CP Ibrahim Adamu Bakori daga Jihar.

Gwamnan Ya yi wannan kira ne a lokacin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata Kano.

Gwamnan ya yi Allah wadai da matakin Kwamishinan da ƴan sandan ya Dauka na janye jami’an tsaro a filin wasa na Sani Abacha inda ake gudanar da bikin ranar samun yancin kai.

Abba ya Kara da cewa a matsayin sa na shugaban Hukumomin Tsaron Jihar, Bai San dalilin janye Jami’an yan sandan cikin kankanin lokacin ba duk da muhimmancin da bikin yake da shi.

Kawo yanzu rundunar Yan Sandan Jihar Kano bata fitar da Wata sanarwa kan dalilin janye Jami’an da kuma rashin ganin Kwamishinan a wajen bikin cikar Nijeriyar Shekaru 65 da aka gudanar a Kano.

Tun bayan ricikin Masarautar Kano aka fara Samun ganin takun Saka Tsakanin gwamnatin Jihar da kuma rundunar Yan Sandan, inda gwamnatin ta Zargi rundunar da kin karbar umarnin ta Zargin da rundunar ta Musanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *