Wike (Tsohon Gwamnan Rivers) ya samo court order kamar yadda APC ta samo court order a Kano don hana yin zabe.
Amman Gwamna Fubara na Rivers ya ce sai ya yi zabe, kuma ya yi zaben, kuma ya rantsar, kuma Ciyamomi suka shiga Ofis.
IGP ya janye Police a Zaben LG na Rivers.
Magoya bayan Wike sukayi amfani da wannan damar suka kulle wasu daga LG Secretariats, suna cewa ba za su bar zababbun Ciyamomi su shiga Ofis ba.
IGP ya sami kalubale sosai bisa hukuncin da ya dauka na janye Police a Rivers.
Bayan matsin lamba IGP ya bada umarni ga Police da su dawo bakin aiki don bada tsaro kuma ya ce a bude LG Secretariats.
- NSCDC Ta Kama Matasan Da Ake Zargi Da Yunkurin Halaka Jami’in Bijilanti A Kano.
- Kotu Ta Umarci Hukumomin Tsaro Su Bayar Da Tsaro A Zaben Kananan hukumomin Kano
A KANO: Gwamnatin Kano ta nada hukumar gudanar da zaben LG. A doka duk mai korafi a lokacin da aka samar da sabon shugabancin hukumar gudanar da zabe, nan ta ke zai gabatar da korafin sa, ba sai an shiga satin da za a gudanar da zabe ba, domin a doka komai yana da lokaci.
APC a Kano ta samo court order don kar a yi zabe duk da cewa doka ce ta ce a yi zabe kuma bisa umarnin Supreme Court dogaro da Constitution.
Duk da haka Gwamnatin Kano ta sami court order ta hana APC duk wani yunkurin hana ta zabe.
Alkalin da ya bada court order na kar a yi zabe tuni aka daukeshi daga Kano amman saboda Siyasa aka dawo da shi Kano, kowa yasan da shi wannan Alkali ake yin siyasar Kano.
Hatsarine babba a shigar da siyasa kotuna.
Hurumin Gowamna A Jiharsa:
1. Gudanar da zaben LG a Jiharsa, kamar yadda Gwamnan Rivers ya cire tsoro ya gudanar da zabe a Jiharsa duk da IGP ya janye Police.
2. Gudanar da Mulki bisa Doka da Adalci akan “State Affairs”.
Daga Barrister Badamasi Suleiman Gandu.