Siyasar Kano na shirin sake zani

Spread the love

Wata dambarwar siyasa ta kunno kai a jihar Kano, inda ake ganin wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar, ciki har da masu rike da mukamai, suna tattauna yiwuwar canza shekar tafiyarsu ta Kwankwasiyya zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Matakin na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan hukuncin kotun ƙolin ƙasar wanda ya bai wa gwamnan NNPP, Abba Kabir Yusuf, nasara a wata shari’a kan halascin zaɓensa.

A halin da ake ciki dai babu ga-maciji tsakanin Jagoran tafiyar siyasar Kwankwasiyya wato Rabi’u Musa Kwankwaso, da Abdullahi Umar Ganduje, shugaban riƙo na jam’iyyar APC kuma jagoran jam’iyyar a Kano.

Batun dai ya soma ƙamari ne bayan an jiyo gwamna Abba Kabir Yusuf, na ta godewa shugaba Bola Tinubu bayan hukuncin da kotun ƙolin Najeriyar ta yanke, da ya tabbatar da halascinsa a matsayin gwamna, duk da zarge-zargen da ya sha yi a baya na cewa ana shirya wata maƙarƙashiya domin ƙwace kujerar tasa.

Kwatsam kuma sai aka ga bullar wasu rahotanni da ke cewa shugaba Bola Tinubu ya ba wa jagororin jam’iyyar ta APC umarnin su je su sasanta da jagoran jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso, aka kuma fara ganin wasu mashawartan Gwamna Abba suna sanye da huluna masu ɗauke da tambarin hular Shugaba Tinubu, har wasu ma sun kai ga sanya tutar jam’iyyar APC a ofisoshinsu.

Injiniya Buba Galadima, na cikin shugabannin jam’iyyar NNPP na Najeriyar, ya kuma yi wa BBC bayanin cewa a siyasance jam’iyyar na iya tattaunaa da kowanne ɓangare, ‘ ‘Yan NNPP da suka fara sanya alamun jami’iyyar APC, ƙila sun zaƙu ne na cewa a yi tafiya tare, amma wanna bai nuna cewa su ne ke riƙe da jam’iyya ko suke riƙe da gwamnati wanda za su iya zartarwa ba’. In ji shi

A cewar Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, shugaba Tinubu ya ba su umarni ne su je su tattauna da dukka masu son shiga jam’iyyar, ba wai su Kwankwaso kaɗai ba, kuma karbar sabobbin ‘yan jam’iyya ba abin da zai jawo tashin hankali ba ne.

Ya ce: ‘Idan gwamnan zai shigo jam’iyyar a bari ya shigo mana, daga nan sai a ga yadda al’amura za su kasance, a ga abin da ya kamata a yi, a ga yadda jam’iyyar ta ke, a ga kuma yadda shi gwamnan ya ke.’

Wani abu da ake ganin na iya haifar da cece-ku-ce tsakanin ɓangarorin idan ta tabbata cewa za su haɗe shine batun jagoranci, da kuma rabon mukamai bisa tsarin siyasa, tuni ma wasu bayanai na yawo cewa za a yi raba dai dai ne, abun da a cewar Injiniya Buba Galadima na NNPP ya ce da kamar wuya:

‘Su muka yiwa aiki ke nan ko? kawai kai ba ka san an yi sassabe ba, ba ka san an yi noma ba, ba ka sanyi girbi ba, ba ka san an kawo amfani gida an dafa tuwo ba, kawai sai ka ce tuwon da aka dafa sai an ba ka rabi?’

Wasu dai na ganin cewa abu ne mai matuƙar wuya waɗannan ɓangarori su iya ajiye rigingimun da ke tsakaninsu su yi aiki tare idan ta tabbata cewa za su haɗe, musamman kan wanda zai zama jagora.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *