Sojar da rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta yi wa ritaya saboda rashin lafiya bayan ta zargi wasu manyan hafsoshi da cin zarafinta ta sake magantuwa.
A watan Janairu ne Ruth Ogunleye ta fito a shafinta na TikTok tana cewa ta sha wahala sanadiyar wasu manyan hafsoshin sojin rundunar.
Zargin nata ya haifar da cecekuce a lokacin, inda ministar mata ta shiga maganar, har ta zanta da babban hafsan soji a lokacin.
Bayan sanar da yi mata ritayar ce Ms Ogunleye ta sake fitowa a wani bidiyon a TikTok, inda ta ce tana so a wallafa sakamakon binciken a duka kafofin sada zumunta domin kowa ya gani.
“A ranar 9 ga Janairun 2024, na fito a kafofin sadarwa na yi ƙorafin cin zarafi da fyaɗen da aka yi mani. Da yadda aka nuna ni da bindiga, aka saka mani ankwa, aka ajiye ni a wani ofis na kwanaki. Ina roƙon rundunar sojin Najeriya ta bayyana sakamakon binciken da ta yi kowa ya gani,” in ji ta.
A ranar Talata ne Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana sakamakon binciken, inda ya ce sun gano wanda take zargi Kanal I.B. Abdulkareem bai aikata laifin ba, sannan ya ƙara da cewa an yanke shawarar yi mata ritaya ne domin rashin lafiya bayan ta ƙi amincewa a duba lafiyarta.