Soji SuN Ragargaji ’Yan Bindiga A Dajin Kaduna

Spread the love

Jiragen Rundunar Sojin sama ta Najeriya sun ragargaza ’yan bindiga da dama a dazukan kananan hukummin Giwa da Igaba a Jihar Kaduna.

Kakakin rundunar, AVM Edward Gabkwet ya ce a ranar Juma’a jiragen yakin suka tarwatsa maboyar wani dan bindiga mai suna Alhaji Layi a yankin Kufan Shantu da ke Karamar Hukumar Giwa.

Jami’in ta ci gaba da cewa a yayin harin, jiragen sun kuma ragargaza ma’adanar kayan amfanin ’yan ta’addan.

Jiragen sun kai makamancin harin a Dajin Malum na Karamar Hukumar Igabi, inda “suka hango ’yan ta’addan sunan kai-komo a sansaninsu, suka tarwatsa shi, suka aika su barzahu.

Edward Gabkwet ya jiragen sojin sun kai hare-haren ne a ci gaba da aikin da suke yi na murkushe ’yan ta’adda a yankin Arewa masu yamma.

Sanarwar da ya sanya wa hannu a ranar Lahadi ta ce, duk da kalubalen da suke fuskanta, sojoji na samun nasara a aikin kakkabe ’yan bindiga a yankinn.

(NAN)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *