Sojoji kaɗai ba za su iya samar da tsaro a ƙasa ba – Janar Chris Musa

Spread the love

 

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce karfin soji kaɗai ba zai samar da tsaron da ake buƙata ba a Najeriya.

Ya ce amfani da karfin soji na bayar da gudummawar kashi 30 cikin ɗari ne kacal na tsaron ƙasa, yayin da kashi 70 ya dogara kan siyasa da kuma tallafi ga walwala da na tattalin arzikin al’umma.

Janar Musa ya bayyana haka ne a wani taro kan tsaron ƙasa da cibiyar daƙile ayyukan ta’addanci karkashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro ya shirya a Abuja.

 

Babban hafsan ya buƙaci haɗin gwiwa wajen daƙile matsalar rashin tsaro a Najeriya.

“Dole ne a haɗa karfi da karfe wajen magance matsalar tsaro, musamman ganin rikice-rikice da kuma rashin tabbas da ya dabaibaye mutane,” in ji shi.

 

Ya ce mutane sun ɗauka cewa sojoji ne kaɗai za su samar da tsaro ba tare da la’akari kan irin gudummawar da kowane ɓangare zai bayar ba wajen tabbatuwar hakan.

Ya ƙara da cewa ƴan jarida ma na da rawar da za su taka wajen tabbatar da tsaro a faɗin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *