Sojoji sun ƙwace aikin sintiri a sassan Bangladesh bayan zanga zanga ta ƙazance

Spread the love

Sojoji na sintiri a kan titunan Bangladesh bayan rikicin da ya ɓalle tsakanin dalibai masu zanga-zanga da ƴan sanda.

Mutane fiye da 100 aka kashe a zanga-zangar ta nuna ƙin jinin gwamnati wadda ta tashi bayan sake ɓullo da tsari ware guraben aikin gwamnati ga iyalan ƴan mazan jiya.

Mutane sun watse a Dhaka babban birnin Bangladeshi, bayan hukumomi sun sanya dokar hana fita da za ta yi aiki har zuwa ranar Lahadi, bayan rikicin da ya ɓalle a ranar Juma’a da dare.

Masu zanga-zangar sun afka gida yarin birnin Narsingdi, inda suka kuɓutar da ɗaruruwan fursunoni.

Shugaban hukumar kula da ƴancin ɗan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya bayyana damuwa kan yadda jami’an tsaro ke amfani da ƙarfin da ya wuce kima a kan ɗalibai masu zanga-zanga, kuma ya ce dole ne su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *