Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar ceto mutum 25 da aka yi garkuwa da su a kudancin Kaduna ranar Laraba bayan fatatttakar ƴanbindiga
Wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na dandalin X, rundunar ta ce an gudanar da aikin mai taken Golden Peace ne domin manoma su samu sukunin girbe gonakinsu, sannan a samar da yanayi mai kyau domin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Daga cikin yankunan da aka yi aikin akwai Ruwan Sanye da Randa da Rafin Gora da Libere Gari da Libere Makaranta da ke ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Haka kuma sojojin sun gano wani ƙaramin asibiti, inda ake jinyar ƴanbindiga idan sun ji raunuka.