Sojoji sun hana yunƙurin ‘ƴan ta’adda’ na kai hari kan kadarorin DSS a Neja

Spread the love

Rundunar sojin Najeriya ta sanar a ranar Laraba cewa ta daƙile yunƙurin ƴan ta’adda a Jihar Neja daga kai hari a kan kadarorin Hukumar DSS.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa PRNigeria cewa sojojin, da taimakon jirgin Super Tucano na sojojin sama sun yi nasarar kashe wasu ƴan ta’addan da suka kai harin.

Majiyar wadda ta nemi a ɓoye sunanta ta ce lamarin ya faru ne a garin Bassa a ƙaramar hukumar Shiroro na jihar.

A cewar majiyar, sojojin sun samu nasara a kan ƴan ta’adda bayan samun bayanan sirri a kan shirinsu na kai harin a kan kayayyakin DSS.

“Nan da nan aka tashi jiragen Super Tucano, inda suka samu nasarar daƙile yunƙurin na ƴan bindigan. Sannan harin jirgin ya kashe aƙalla ƴan bindiga 30,” inji majiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *