Sojoji sun karyata zargin nuna son kai a rikicin Mangu

Spread the love

Rundunar sojin Najeriya sun musanta zargin nuna son kai da ake yi musu a rikin ƙaramar hukumar Mangu na jihar Plateau.

Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran rundunar Birgediya Janar Tukur Gusau, ya ce bidiyon da shugaban ƙungiyar Kiristocin Najeriya CAN, Reverend Timothy Daluk, ya yi, da ke zargin jami’an sojin da ake aiki domin kwantar da rikicin da ya ɓarke a yankin na nuna son kai.

Sanarwar ta ce zarge-zargen da ke cikin bidiyon na ce sojojin na goyon bayan wani ɓangare a rikicin, ba su ta tushe balle makama.

A ranar 23 ga watan Janairu ne wani rikici ya ɓarke a ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta tsawon kwana guda.

An kuma tura jami’an soji da ke aiki da rundunar Operation SAFE HAVEN mai yaƙi da ‘yan bindiga zuwa yankin domin tabbatar da bin dokar tare da maido da kwanciyar hankali da kuma daƙile bazuwar rikicin zuwa wasu sassan jihar.

Birgediya Tukur Gusau ya ce dakarun sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata cikin ƙwarewa da bin tsarin doka, Inda suka samu nasarar kama wasu daga cikin waɗanda ke da hannu a rikicin da ya yi sanadin ɓarna da ƙona dukiyoyi tare da da ƙwato makamai.

Kotu ta aike da yar Tiktok Ramlat Princess gidan gyaran hali bisa zargin yada badala

An karrama yan sanda huɗu saboda ƙin karɓar cin hancin miliyan 8.5 a Taraba

“Amma abin takaicin shugaban addini, wanda ake tunanin zai nuna halin gaskiya da adalci wajen hana bazuwar ƙarairayi kan sojoji”, in ji Janar Gusau.

Ya ƙara da cewa “Muna son jaddada cewa sojoji ba sa ɗaukar ɓangaranci, kuma suna mayar da hankali wajen gudanar da aikinsu kamar yadda kundin tsaron mulki ya tanadar na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, za mu ladabtar da duk wanda aka samu da saɓa dokar ƙasa ba tare da son rai ko ɓangaranci ba”.

Daga ƙarshe ya gargaɗi duka ‘yan ƙasar da ke yi wa sojoji irin waɗanna zarge-zarge da su daina, ko su ɗanɗana kuɗarsu duk kuwa da irin matsayin da suke da shi a cikin al’umma.

Ya ce irin waɗanna zarge-zarge ba za su sanyaya musu giwwa ba a ƙoƙarin da suke yi na kawar da duka nau’ikan fitintinu a faɗin ƙasar.

Ya kuma yi kira da ‘yan ƙasar da su ci gaba da mara wa sojojin ƙasar baya a ƙoƙarinsu na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *