Sojoji sun kashe kwamandan IPOB a Imo

Spread the love

Bayan yunƙurin ƴan bindiga na kafa sansanoni a jihar Imo, sojojin Najeriya sun gudanar da wani aikin sharan fage a ranar 6 ga Mayun 2024 inda suka tarwatsa wata maɓuyar ƴan bindigar.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta fitar a shafinta na X, jami’anta sun gudanar da ayyukan ne a yankunan Udda da Ihittukwa da kuma Orsumoghu a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo, bayan samun bayanan sirri.

Sanarwar ta ce ƴan bindigan sun yi amfani da abubuwa masu fashewa a lokacin artabu da sojoji sai dai daga ƙarshe sojojin ne suka yi nasara.

A lokacin farmakin an kashe mutum huɗu daga ɓangaren ƴan ƙungiyar ta IPOB, ciki har da wani kwamandan kungiyar, Tochukwu wanda aka fi sani da Ojoto.

An kuma samu nasarar kwace makamai da dama daga maboyar, waɗanda suka hada da bindigogi da bama-bamai da dai sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *