Sojoji sun kashe masu tsattsauran ra’ayi a Taraba

Spread the love

A kokarinta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Taraba, runduna ta shida ta sojojin Najeriya da ke jihar Taraba ta kashe ,masu tsattsauran ra’ayi biyar, tare da dakile yunkurin satar mutane da kuma kwace makamai da dama.

Rundunar ta ce ta samu bayanan sirri a kan shirin da wasu masu tsattsauran ra’ayi ke yi na sace mambobin wani coci a yayin da suke komawa gida da ga wani taro da suka yi a kan hanyar Wukari zuwa Tor-Tse da kuma Takum.

Rundunar mai yawan sojoji 93 da aka tura Wukari, ta yi kokari wajen dakile yunkurin mutanen.

Da farko rundunar ta yi taho mu gama da masu tsattsauran ra’ayin inda a nan ne ta yi nasarar kashe mutanen hudu da kuma gano bindiga 2 samfurin AK 47 da kananan bindigogi da sauran makamai.

A wani labarin mai da wannan kuma, a ranar 27 ga watan Maris din 2024, sojoji sun yi arangama da wadanda ake zargi masu tsattsauran ra’ayi ne a kusa da garin Chancan da ke karamar hukumar Takum.

A yayin arangamar sojojin sun yi nasarar kashe daya daga cikin masu tsattsauran ra’ayin ta re da kwace makamai da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *