Sojoji Najeriya da ke yaƙi da ƴanbindiga a arewa maso yammacin Najeriya sun ce sun kashe wani babban mataimakin gawurtaccen ɗanbindigar nan da ke addabar yankin, Bello Turji, mai suna Aminu Kanawa.
A wata sanarwa da sojojin suka fitar ta ce dakarun dai “sun samu nasarar kashe Aminu Kanawa ne lokacin wani samame da suka kai a duwatsun Fakai da ke ƙaramar hukumar Shinkafi.”
“Ɗanbindigar ya yi ƙaurin suna ne wajen addabar al’ummar ƙananan hukumomin jihar ta Zamfara da ma Sokoto da suka haɗa da Zurmi, Shinkafi, Isa da Sabon Birni.”
Sanarwar ta ƙara da cewa baya ga Aminu Kanawa da suka kashe, sojojin sun jikkata ƴanbindiga irin su Dosso wanda ƙanen Turji ne da kuma Danbokolo wanda shi ma makusancinsa ne.
Har wayau, sanarwar ta ƙara da cewa a wani sabon harin da dakarun suka kai sun samu nasarar kashe manyan kwamandojin Bello Turji kamar haka:
Abu Dan Shehu
Jabbi Dogo
Dan Kane
Basiru Yellow
Kabiru Gebe
Bello Buba
Dan Inna Kahon-Saniya-Yafi-Bahaushe,
Rundunar sojojin kamar yadda sanarwar ta ce ta samu damar kashe ƙarin kwamandojin Turji guda 24 da ke ƙoƙarin tserewa daga sansanin Turjin da ke Geɓe da Isa.
Sanarwar ta kuma ce dakarun sun kuma kashe wani ɗanbindiga wanda makusancin Halilu Sububu ne yayin kai farmaki a maɓoyar Bello Turjin, mai suna Suleiman.
Daga ƙarshe sanarwar ta ce samun nasarar kashe ƴanbindigar waɗanda ƙasurgumai ne babban rashi ne ga Bello Turji wanda “nan gaba kaɗan zai zama cikin komarmu”.
Kafar watsa labarai ta PR Nigeria ta wallafa cewa wata majiya daga hedkwatar tsaro ta Najeriya ta tabbatar mata da tserewar Turji zuwa yankin Maradun, sannan mutanen yankin sun tabbatar da ganin wasu babura suna zarya, waɗanda ake tunanin sun ɗauki ƴanbindiga da aka harba ne suna tafiya da su zuwa yankin Kadanya da Bayan Ruwa.
Ko a ranar Talata sai da sojojin suka bayar da sanarwar kashe ɗangidan Bello Turji yayin wani samame da suka kai sansanin ɗanbindigar.