Dakarun Najeriya shiyya ta bakwai, sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP da na Jama’atul Ahlis Sunnah Wal Jama’a guda biyar, tare da ceto mata da yara 78 a wasu kauyuka a jihar Borno.
Wata sanarwa da sojojin suka fitar, ta ce dakarunta sun samu nasarar ce bayan samame da suka kai maɓoyar mayakan ISWAP da JAS a arewa maso gabas.
“A wani samame da aka gudanar ranar Juma’a 22 ga watan Maris 2024, sojoji sun samu nasarar tartwatsa wasu kauyuka shida waɗanda ƴan ta da kayar-baya suke zaune tare da mutanen da suka yi garkuwa da su,” in ji sanarwar.
Sojojin sun ce yayin samamen, sun yi musayar wuta da ƴan ta’addan, kafin daga bisani su cimmusu tare da kashe biyar daga cikinsu.
Sanarwar sojojin ta ce cikin mutanen da aka ceto sun haɗa da mata 35 da kuma yara 43 waɗanda ƴan ta da kayar-bayan suka yi garkuwa da su.
Muna samun nasara a yaki da masu aikata laifuka – Sojin Najeriya