Sojoji Sun Kashe Wani Dan Bindiga Da Yaransa 5 A Kaduna

Spread the love

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar halaka wani gawurtaccen ɗan bindiga da ta jima tana nema a jihar Kaduna.

Rundunar ta ce ta halaka shi ne yayin da yake tafiya da wasu muƙarrabansa, bayan wasu bayanan sirri da ta samu, lamarin da ya sa ta tura dakarunta domin artabu da su.

Kakakin rundunar sojin saman Air Vice Mashal Edward Gabkwet, ya yi wa BBC ƙarin bayani, a ranar Lahadi, inda ya ce an kashe mutumin ne, Mustapha Abdullahi, tare da wasu mutum biyar cikin yaransa, bayan da aka samu bayanan sirri kn zirga-zirgarsu a kusa d dajin Sabon Gida, da ke kan hanyar Sabon Birni a ƙarmar hukumar Igabi ta jihar ta Kaduna.

Ya ce, ”bayan da aka tura jami’an sojin saman ne su bincike yankin, suka haɗu da ‘yan bindigar da ke kan babura, inda suka yi musayar wuta da su, inda sojin suka halaka su gaba daya.

AVM Gabkwet, ya ce kayan da aka samu a wajen ‘yan ta’addar sun haɗa da bindigar gargajiy t maharba guda biyar, da bindiga mai sarrafa kanta kirar gida da harsasai da layu da ƙyastu (na kunna wuta) da layikan waya da kuma rigar wayoyin hannu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *