Sojoji sun kashe ƴan bindiga a jihar Taraba

Spread the love

Sojojin Najeriya daga runduna ta shida sun kashe ƴanbindiga biyu a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Bali da ke jihar Taraba.

Rundunar ta ce sojojinta ne suka kai samamen bayan samun bayanan sirri game da kasancewar ƙungiyoyin ƴanbindiga a yankunan Nayinaya da Garin Daniel da Garbatau.

A cewar rundunar, sojojin sun yi fito na fito da ƙungiyoyin ƴanbindigar inda suka yi nasarar kashe biyu daga cikin su tare fa ƙwato muggan makamai – bindigogi da kuma alburusai.

Najeriya da wasu kasashen Afirka sun fuskanci matsalar katsewar internet

Yan Jaridar Portugal Sun Fara Yajin Aiki Karon Farko Cikin Shekaru 42.

Rundunar ta ce tana ci gaba da gudanar da aiki tuƙuru domin fatattakar ƴanbindiga da masu aikata miyagun laifuka a jihar har sai an samar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Kwamandan runduna ta shidan ya yaba wa sojojin bisa ƙoƙarin da suka yi inda kuma ya yi kira ga jama’a da su samar da bayanai a-kai-a-kai da za su kai ga murƙushe miyagu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *