Sojoji sun kuɓutar da mutum 35 tare da kashe ƴan bindiga biyu a Katsina

Spread the love

Rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) ta ce ta yi nasarar kashe ƴan bindiga biyu a jihar Katsina tare da kuɓutar da wasu mutum 35 da aka yi garkuwa da su a wani samame da sojojin suka yi a jihar a ranar 27 ga watan Janairu.

Kakakin Rundunar, Kyaftin Yahaya Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Ya bayyana cewa wasu ‘ƴan ta’adda’ da dama sun tsere da raunukan harbin bindiga.

Yadda sojin Najeriya suka yi wa ƴanbindiga ruwan wuta ta sama

Rundunar yan sandan Kano ta magantu kan farwa jami’in lafiya da yan uwan mara lafiya suka yi a asibitin kwararru na Murtala Muhammed

Sanarwar ta kara da cewa “A yayin farmakin, sojojin sun yi arangama da masu ɗauke da makamai, inda suka kashe biyu daga cikinsu yayin da wasu suka tsere da mummunan raunin bindiga.”

“A ci gaba da gudanar da ayyukan share fage na lokaci guda a yankunan da ke da alhakin gudanar da ayyuka a jihar wanda ya ci gaba da samun gagarumar nasara, dakarun rundunar hadin gwiwa ta operation hadarin daji da ke aiki a jihar sun ceto mutane 35 da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu ‘yan ta’adda biyu a jihar Katsina a wani samame da suka kai.”

Ya ce waɗanda aka ceto sun haɗa da maza 19 da mata 12 da kuma yara huɗu, ya ce nan take kwamandan rundunar, Birgediya Janar Oluremi Fadairo ya miƙa su ga gwamnatin jihar Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *