Sojoji sun kuɓutar da mutum uku da akayi garkuwa da su a jihar Taraba

Spread the love

Sojojin Bataliya ta 114 (Rear) na 6 Brigade na Sojojin Najeriya sun ceto wasu mutane uku da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jalingo babban birnin jihar Taraba.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 6 Brigade, Leiutenant Olubodunde Oni ya fitar wa manema labarai.

Sanarwar ta ce sojojin sun yi aiki ne da bayanan sirri game da tafiyar ‘yan bindigar tare da waɗanda suka sace daga Ardo-Kola zuwa Yoro, sannan suka tura dakaru a kauyen Apawa da ke karamar hukumar Yoro zuwa yankin tare da fatattakar ‘yan bindigar.

An kama masu garkuwa da mutane 5, a Dajin Ivu dake Imo

Ya kara da cewa sojojin da ke nuna kwarewa da jajircewa sun fafata da ƴan bindigan da karfin wuta wanda hakan ya tilasta musu yin watsi da mutanen uku da suka sace.

Oni ya ce “Mun yi farin cikin bayar da rahoton cewa mutanen da aka ceto sun hadu da iyalansu yayin da muke ci gaba da bin sawun masu garkuwa da mutane.”

“Wannan aikin ya nuna jajircewar rundunar na tabbatar da tsaro da jin dadin mazauna jihar Taraba.”

Ya yi kira ga hukumomi da ’yan kasa masu bin doka da su “da su ba da goyon baya ga wannan kokarin ta hanyar samar da sahihin bayanai don taimaka wa sojoji a aikinsu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *