Sojoji sun sake buɗe rukunin shagunan Banex a Abuja

Spread the love

Rundunar sojin ƙasan Najeriya ta tabbatar da sake buɗe rukunin shagunan kasuwanci na Banex da ke unguwar Wuse 2 a Abuja bayan rufe su da aka yi sakamakon wata tashin-tashina, a ranar Asabar, 18 ga watan Mayu, 2024.

Ranar Lahadi ne kuma 19 ga wata, rundunar sojin ta rufe wajen ne domin gudanar da bincike kan ayyukan da ta bayyana a matsayin na masu aikata ɓarna.

Kafin rufewar an ga wani bidiyo na yawo a shafukan intanet inda wasu mutane suka far wa wasu sojoji a kusa da rukunin shagunan.

Bidiyon ya nuna yadda wasu jami’an ƴansanda suka shiga tsakani domin ceton jami’an sojin da mutane suka riƙa kai wa duka da jifa.

Da yake sanar da sake buɗewar a wata sanarwa a yau Litinin, Darektan hulɗa da jama’a na rundunar sojin Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce matakin sake buɗewar na daga cikin matsayar da aka cimma a taron da aka yi a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, da shugabannin rukunin shagunan da sauran shugabannin hukumomin tsaro na Abuja.

Janar Onyema, ya ce daga cikin matakan da aka ɗauka a taron har da rufe shago mai lamba C93, da kuma kama masu shagon da aka yi rikicin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *