Sojoji sun tarwatsa sansanin ƙasurgumin ɗan fashin daji a Zamfara

Spread the love

sojin Najeriya ta ce dakarunta da ke aikin dakile ayyukan ta’addanci sun kai samame tare da tartwatsa sansanin wani kasurgumin dan fashin daji mai suna Yellow Janbros a kauyen Dangunu da ke karamar hukumar Maru na jihar Zamfara.

Sanarwar da sojojin suka fitar a shafin X, ta ce sun samu nasarar kashe wani da suka kira ɗan ta’adda yayin samamen.

Sojojin sun ce ɗan fashin dajin ya kware wajen yin garkuwa da mutane da kuma aikata ta’addanci a sassan arewa maso yamma yayin samamen da suka kai ranar Litinin, 8 ga watan Afrilun 2024.

“Sojojin sun ci karfin ‘yan fashin dajin inda suka samu nasarar kashe daya daga cikinsu,” in ji sanarwar sojojin.

Sun kuma ce sun kwato makamai da suka haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya, da harsasai da kuma buhunan hatsi 150 da ‘yan bindigar suka sace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *