Dakarun haɗin gwiwa na jami’an tsaron Najeriya da ke aikin soji na musamman wato Operation Fansan Yamma sun ce sun samu nasarar fatattakar ƴanbindiga daga yankin Tudun Bichi da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta jihar Katsina.
A wata sanarwa da Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce sun samu nasarar ne bayan samun bayanan sirri game da ayyukan ƴanbindigar a yankin.
Ya ce, “a farmakin haɗin gwiwa da dakarunmu suka kai, bayan jirgin sama ya tarwatsa su, sai suka sake haɗuwa a wani gefen, inda nan kuma sojojin ƙasa suka gwabza da su, kafin suka arce.
Ya ce jirgin sama ya bi su a baya yana buɗe musu wuta, inda ya ce ƴan ƙauyukan yankin sun tabbatar musu da mutuwar wasu daga cikin ƴanbindigar, tare da raunata wasu manyan ƴanbindiga irin su Manore da Dpogo Nahalle.
- An Ba Wa Yan Kasuwar Kwanar Gafan Wa’adin Mako Guda Su Tashi
- Harin Jiragen Sojojin Nigeria Ya Kashe Mutane 10 A Sokoto