Sojojin DR Kongo sun ce sun daƙile yunƙurin juyin mulki a ƙasar

Spread the love

Rundunar sojin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar kongo sun ce sun daƙile juyin mulkin – da wasu ‘yan ƙasar da na ƙetare suka yi yunƙurin yi wa – shugaban ƙasar Felix Tshikedi a Kinshasa, babban birnin ƙasar.

Cikin wani jawabi da ya ta gidan talbijin na ƙasar, mai magana da yawun sojojin ƙasar Burgediya Janar Sylavin Ekenge, ya ce a yanzu ƙura ta lafa, kuma sojojin ƙasar na tsare da wasu da ake zargi da hannu a lamarin.

Jawabin nasa na zuwa ne sa’o’i bayan da wasu mutane ɗauke da makamai suka afka gidan tsohon shugaban ma’aikata kuma babban aminin shugaban ƙasar, da safiyar ranar Lahadi.

Shaidu sun ce ga wasu mutane kimanin 20 sanye da kayan sojoji sun afka wa gidan sannan suka ji ƙarar harbe-harben bindiga.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce maharan mambobin wata ƙungiya ce da ake kira ‘New Zaire Movement’ mai alaƙa da ɗan siyasar ƙasar da ke zaman gudun hijira a ƙetare, Christian Malanga.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar masu gadin gidan biyu da mahari guda.

Kawo yanzu shugaban ƙasar Felix Tshisekedi bai ce komai ba game da batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *