Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta amsa cewa jirginta ne ya kai harin bom a kan masu taron Mauludi a Jihar Kaduna.
Babban Kwamandan Rundunar Sojin Kasa ta Daya da ke Kaduna, Manjo-Jananr VU Okoro ya bayyana cewa jirginsu ne ya yi kuskuren kai hari a kan fararen hula da lokacin da yake tsaka da aikin yaki da ’yan ta’adda.
Ya sanar da haka ne a taron gaggawa na majalisar tsaron jihar da Mataimakiyar Gwamna, Hadiza Balarabe Sabuwa ta jagoranta bayan aukuwar lamarin.
Aminiya ta ruwaito ana fargabar mutane akalla 30 sun mutu a sakamakon harin bom din da jirgin sojin ya kai wa masu taron mauludin a ranar Lahadi da dare.
Wani mazaunin yankin Tumbin Biri, inda aka kai harin a Karamar Hukumar Igabi ya shaida wa Aminiya cewa suna tsaka da taro wani jirgi ya jefo musu bom.
An tsananta tsaro a wasu ƙananan hukumomin Kaduna saboda zaɓe
Kungiyar lauyoyi NBA ta kai karar Hannatu Musawa kan shedar bautar ƙasa NYSC
Sanarwar da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar bayan taron gaggwar majalisar tsaron jihar ta ce ana ci gaba da aikin ceto a wurin da abin ya faru.
Aruwan ya kara da cewa wadanda suka samu raunuka kuma an kai su Asibtin Koyarwa na Barau Dikko domin duba lafiyarsu.
Tun da farko bayan fitar rahoton harin, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta musanta cewa jirginta ne ya kai farmakin, don haka a kara bincikawa.