Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun da ta tura don aikin murƙushe ‘yan ta-da-ƙayar-baya a jihohin Katsina da Zamfara sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga 11 a cikin kwana biyu.
Sun dai kai samame ne maɓoyar waɗanda suka kira ‘yan ta’adda, inda suka kashe wani adadi na ‘yan bindigar a ranar 29 ga watan Maris.
Ta ce dakarun soji sun yi nasarar kai wa mafakar wani riƙaƙƙen ɗan fashin daji mai suna Hassan ‘Yan tagwaye hari, a cikin ƙaramar hukumar Tsafe, inda suka kashe uku a cikinsu tare da ƙwato makamai.
Rundunar sojin ta kuma ce dakarunta sun ragargaza sansanonin ɗan fashin, wanda ta ce yana da hannu wajen satar mutane da ayyukan ta’addanci a wasu yankuna na arewa maso yamma.
A jihar Katsina kuma, cewar rundunar sojin ƙasan Najeriya, dakarunta sun gwabza faɗa a ranar 30 ga watan Maris da waɗanda suka kira ‘yan ta’adda a Shawu Kuka da Shinda da Tafki da Gidan Surajo da Citakushi da Kabai I da Kabai II duka a cikin ƙaramar hukumar Faskari.
Ta ce dakarun sun yi nasarar kashe ‘’yan ta’adda’ takwas tare da gano bindigogi ƙirar gida guda uku da kakin sojoji da kuma ɗumbin hatsin sata.