Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin sace mutane a Benue

Spread the love

Dakarun sojin Najeriya da aka tura domin yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa ta tsakiya tare da hadin gwiwar jami’an sa-kai, sun yi nasarar dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane tare da ceto wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a jihar Benue.

Sojojin sun yi gaggawar kai ɗauki bayan amsa kiraye-kiraye daga sansanin ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a kauyen Tsede da ke kan titin Tor Donga Takum a ƙaramar hukumar Katsina Ala, a jihar, inda suka yi artabu da masu garkuwa da mutane, lamarin da ya tilasta musu yin harbi.

Mutanen da aka ceto waɗanda suka haɗa da wani Cif Sano Kursi da Augustine Sada, ba su samu wani rauni ba, kuma tuni aka hada sada su da iyalansu.

Sojojin sun kuma ƙwace makamai da alburusai wanda ya nuna jajircewar sojoji wajen kare rayuka da dukiyoyi da kuma muhimmiyar rawar da jami’an tsaro da al’umma ke takawa wajen yaki da miyagun laifuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *