Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun sami nasarar halaka mutum fiye da 100 a sassan kasar, wadanda ake zargin ƴan ta’adda ne, sun kuma ce sun kama 172 da ransu, an ƙubutar da mutum 214, da aka yi garkuwa da su, tare da ƙwato makamai da dama.
Mataimakin daraktan watsa labaran hedikwatar tsaron, Guruf Kyaftin Ibrahim Ali Bukar, ya shaida wa BBC cewa, a wannan makon nan sun samu nasarar ne duk da tsakon da zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi a ƙasar.
Guruf Kyaftin Ibrahim Ali ya ce an samu nasarar ne a jihohin Kaduna da Neja da Zamfara da Borno da Yobe, “Da kuma can Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, inda arziƙin man Najeriya yake, an kama ɓarayin mai 32,wadanda za su iya sace man da ya kai darajar sama da naira biliyan ɗaya.”
Rundunar sojin ta Najeriya ta ce ta kama makamai kusan 66, ciki har da bama-bamai da bindigogi kirar AK47, da harsasai sama da 4,000
Duk da irin wannan nasara da jami’an tsaron Najeriya ke cewa sun samu, ana ci gaba da samun hare-haren ƴan bindiga a arewacin ƙasar da satar mutane domin ansar kuɗin fansa, sai dai kan hakan Guruf Kyaftin Ibrahim Ali ya ce “Idan dambu ya yi yawa baya jin mai, amman haƙiƙanin gaskiya ana ƙoƙari, kuma za a ci gaba da ƙoƙari.”
Rundunar sojin ta yi kira ga ƴan ƙasar da su riƙa taimaka mata da bayanan sirri, “wato idan ka ga waɗannan mugayen suna shirya wani abu ko suna ɓoye a sanar da sojoji, domin mu je mu daƙile su, domin yaƙin namu ne gaba ɗaya ƴan Najeriya.”
Sai dai duk da wannan nasara da jami’an tsaron ke cewa suna yi kan ƴan fashin dajin, al’ummar yankin na arewa maso yamma na ci gaba da kokawa kan yadda lamarin ke ƙara ƙamari.