Dakarun sojojin Najeriya sun ce sun kama wasu mutane 8 da suka ƙware wajen safarar man fetur daga Najeriya zuwa ga ƴan tawayen Ambazoniya a Jamhuriyar Kamaru.
Rundunar sojin Najeriya ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a inda ta ce an kama mutanen ne a kan hanyar Abong-Kurmi Baissa a jihar Taraba, a kan iyakar Najeriya da Kamaru.
A yayin gudanar da bincike, waɗanda ake zargin sun amsa laifin safarar man fetur da kuma sayar da man ga ƴan tawayen Ambazoniya na Kamaru, waɗanda aka hana su shiga Najeriya don siyan kayan kai tsaye.
A lokacin da aka kama su, waɗanda ake zargin suna tafiya ne a cikin motoci ƙirar J5 guda uku, ɗauke da jarkoki 605, kowace jarka shaƙe da lita 40 kuma darajar man da suke dauke da shi ya kai naira 19,360,000.
Binciken da aka yi ya kai ga gano wasu ƴan ƙungiyar masu safarar man fetur ɗin, ciki har da jagoransu.
- An ƙaddamar sabon a-daidaita-sahu na mata zalla a Kano
- Ana Zargin ’Yan Najeriya Da Satar N720m A Wurin Aikinsu