Sojojin Najeriya sun kama masu safarar bindigogi biyar a Filato

Spread the love

Dakarun sojin Najeriya sun ce sun kama mutum biyar waɗanda suka shahara wajen safarar bindigogi a jihar Filato tare kuma da ƙwato makamai.

Wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na sojojin Manjo Stephen Zhakom ya fitar ranar Talata, ya ce an samu nasarar ce bayan wani aikin samame da suka kai jihar, inda ya ce hakan na cikin zimmar sojoji na ganin sun kakkaɓe masu rike da makamai ba bisa ka’ida ba.

“An fara samamen da dakarun Operation Safe Haven suka yi tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro ne a ranar Litinin da daddare har zuwa safiyar yau Talata,” in ji shi.

Ya ce dakarun sun yi wa maɓoyar wani mai safarar bindigogi mai suna Mohammed Sani a garin Naraguta kan hanyar Bauchi zuwa Jos, inda nan ne kuma suka yi nasarar kama shi tare da wasu mutum huɗu.

Makamai da sojojin suka kwace sun haɗa da bindigar AK-47 guda biyu, alburusai da sauransu.

Zhakom ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan mutanen da aka kama d anufin ƙara samun bayanai da za su kai ga kama sauran masu harkar domin daƙile aikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *