Sojojin Najeriya sun kama waɗanda ake zargi da sace ƙarafunan layin dogo

Spread the love

Rundunar sojin Najeriya da ke aiki da runduna ta ɗaya da ke jihar Kaduna sun kama mutum 47 bisa zargin ɓarnatar da layin dogo.

Mai riƙon muƙamin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Musa Yahaya ne ya bayyana haka ranar Asabar a Kaduna.

Laftanar Kanar Yahaya ya ce dakarun rundunar sun kama mutanen ne a lokacin wani samame da suka kai unguwannin Kakau Daji da Anguwan Ayaba da ke yankin ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna, ranar 26 ga watan Yuni.

Ya ce an kama mutanen ne lokacin da suka loda mota biyu na ƙarafunan layin dogon da suka sata.

Jami’in sojin ya ce waɗanda ake zargin sun bayyana wa sojojin cewa wani mutum ne mai suna Alhaji Babawo ke sanya su aikin sace ƙarafunan.

Najeriya – wadda a baya-bayan nan ke ƙoƙarin farfaɗo da sufurin jiragen ƙasa – na fama da matsalolin sufurin jiragen, inda a lokuta da dama wasu mutane ke ɓarnatar da titin jirgin ta hanyar sace ƙarafunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *