Dakarun sojin Najeriya da aka tura jihar Zamfara domin yaƙar ta’addanci sun kashe shahararren jagoran ƴan bindiga mai suna Junaidu Fasagora tare da wasu mayaƙansa, a cewar rundunar.
Wata sanarwa da ta wallafa a intanet ta ce sun yi nasarar ce bayan fafatawa da kuma musayar wuta mai zafi a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
“Junaidu Fasagora tare da sauran ƴan bindiga abokansa sun dade suna garkuwa da mutane tare da aikata wasu ayyukan ta’addanci ga al’ummar jihohi da dama na yankin arewa maso yammacin kasar,” in ji sanarwar.
- Jami’ar Khalifa Isiyaka Rabi’u, Ta Yaba Wa Kwamishinan Yan Sandan Jahar Kano
- Ana neman mutum takwas da ake zargi da kisan sojin Najeriya 17
Ta ƙara da cewa kawar da su “wata gagarumar nasara ce a yaƙin da ake yi da ta’addanci da kuma rashin tsaro”.
Mutuwar Fasagora na zuwa ne yayin da ake ci gaba da raɗe-raɗin mutuwar shahararren ɗan fashin daji Dogo Gide, wanda har yanzu BBC ba ta kai ga tabbatar da mutuwarsa ba.