Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga da lalata mafakarsu a Kaduna

Spread the love

Dakarun sojojin Najeriya da aka tura domin yaki da ta’addanci a jihar Kaduna sun kashe wasu ƴan bindiga tare da dakile ayyukansu a karamar hukumar Giwa da ke jihar.

A wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumuntata na X, rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kai farmakin ne a sansanin ƴan bindiga da ke kauyen Basurfe da ke kudu maso yammacin Kidandan, bayan da wasu bayanan sirri suka tabbatar da cewa wasu ‘ƴan ta’adda’ na amfani da ƙauyen a matsayin mafakar gudanar da ayyukansu.

Sanarwar ta ƙara da cewa a yayin da sojoji suka tunkari ƙauyen, ƴan bindigan sun yi musu kwanton-ɓauna amma sojojin sun yi nasarar tarwatsa su

A yayin zazzafar arangama ne sojojin suka hango wasu daga cikin ‘ƴan ta’addar’ suna yunkurin tserewa daga yankin a kan babura, inda suka yi nasarar fatattakar su tare da kashe mutum biyu daga cikin su – in ji sanarwar.

Sojojin sun kuma ƙwace makamai da dama har da babura guda biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *