Sojojin Najeriya sun kashe kasurgumin dan fashi a Kaduna

Spread the love

Jami’an tsaron Najeriya sun yi nasarar kashe wani ɗan bindiga da aka fi sani da Boderi Isyaku.

Rahotanni sun ce an kashe shugaban ‘yan bindigar ne da wasu mayakan sa a wani artabu da dakarun sojojin Nijeriya, a yankin Bada/Riyawa da ke ƙananan hukumomin Chikun da Igabi na jihar Kaduna.

Boderi ya shafe kusan shekara goma yana gudanar da munnan ayyuka yankunan a jihohin Kaduna da Neja, ta hanyar kai hare-hare, da kuma garkuwa da mutane.

Majalisar dattawa Najeriya ta amince kafa kwamitin kudi na CBN

Ba mu da labarin buhun siminti ya kai 15,000 a Kasuwa : Fatima Dangote

An alaƙata shi da kai hare-hare da dama a yankunan da suka haɗa da Sabon Birni da Rigasa da Buruku da Rijana da Kateri da hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

An kuma zarge shi da ƙulla alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci, tare da haɗa kai da su wajen kafa sansanoni a waɗannan yankunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *